By: Kamal Yalwa – Ningi, Bauchi
Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Danyaya III, ya kaddamar da wani babban kwamitin yaki da sare daji ba bisa ka’ida ba, musamman don hana sare bishiyoyi domin gawayi da katako.
Kaddamarwar ta gudana ne a Fadar Ningi, inda Sarkin ya bayyana cewa kwamitin zai fara aiki nan take, domin kawo karshen irin wannan barna da ke haddasa dumamar yanayi da lalata muhalli.
A cewar Sarkin, aikin kwamitin zai mayar da hankali ne wajen hana sare dajin da ba bisa ka’ida ba, yaki da gawayi da katako har da gudubale, wato sare bishiyoyi don sarrafa su.
Sarkin ya kara da haramta sare wasu bishiyoyi na musamman kamar su Tsamiya, Dorawa, Kanya Dinya da Tabo, ko da kuwa bishiyar tana cikin gidan mutum ne.
Ya bayyana cewa duk wanda aka kama da karya wannan doka zai gurfana a gaban kwamitin, kuma ba za a yi wasa da batun ba.
Tarkon Kwamitin ya kunshi:
- Sarkin Ningi, Alh Haruna Yunusa Danyaya III – Shugaban kwamitin
- Shugabannin kananan hukumomi na Ningi da Warji – Mataimakan shugabanni
- Hakimai – Shugabannin kwamitin a yankunansu
- Daraktan aikin gona na Warji, Shugaban ma’aikatan Fadar Ningi, DPO na Ningi, Warji da Burra, jami’an Civil Defence da DSS daga Ningi da Warji, da Matawallen Ningi.
Sakataren kwamitin shine Alhaji Ibrahim Aliyu Halad, Daraktan sashin aikin gona na Karamar Hukumar Ningi.
Sarkin ya ja kunnen jama’a da su guji yin kunnen uwar shegu da wannan sabuwar doka, yana mai cewa ba za a lamunci cin zarafin muhalli ba a masarautar Ningi.
